Mun yi wa ƙudirin haraji karatu na biyu don kwamiti ya samu damar bibiyarsa – Sanata Barau

Spread the love

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau I Jibril ya ce Majalisar Dattawan ƙasar ta yi wa ƙudirin haraji karatu na biyu ne domin a samu damar miƙa shi ga kwamitin kuɗi domin bibiyarsa da faɗaɗa nazari a kansa.

Cikin wata hira da BBC Sanatan mai wakiltar Kano ta Arewa ya ce majalisar ta bayar da shawarar miƙa wa kwamitin kuɗi ya duba tare da shirya jin ra’ayin jama’a, kuma hakan ba zai yiwu ba har sai an yi wa ƙudirin karatu na biyu.

”E an ji an yi jawabai, kuma mu a nan majalisa za mu iya tambayarsu, amma ‘yan Najeriya ba za su samu damar yin tambaya game da ƙudirin ba har sai an kira jin ra’ayin jama’a”.

Sanata Barau ya ce dokar haraji ba za ta tabbata ba dole sai da masu ilimin haraji, ”kan haka ne yanzu aka tura domin su je su duba, su feɗe komai sannan su yi mana bayanin abin da ya ƙunsa”.

Ƙudirin harajin – da majalisar dattawan ta yi wa karatu na biyu a makon nan – ya haifar da ce-ce-ku-ce musamman tsakanin wasu ‘yan arewacin ƙasar, da ke zargin cewar ƙudirin zai cutar da yankin.

To amma mataimakin shugaban majalisar ya ce karatu na biyu ba shi ke nuna cewa majalisar ta amince da ƙudurin ba, ”ai a nan ne ma aikin yake farawa”.

Ana ci gaba da tattaunawa tare da nuna yatsa tun bayan da ƙudurin dokar haraji da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike wa majalisar dokokin ƙasar domin yin muhawara a kansa ya tsallake karatu na biyu a ranar Alhamis.

Ƙudurin – wanda ke ci gaba da janyo taƙaddama tsakanin ƴan ƙasar – gwamnatin ƙasar na ganin cewa zai taimaka wajen inaganta tattalin arzikin Najeriya.

An dai yi zazzafar muhawara a zauren majalisar dattawan ƙasar a ranar ta Alhamis tsakanin masu goyon bayan ƙudirin da masu adawa da da shi – da suka riƙa kiraye-kirayen watsi da shi.

Ƙudurin ya fuskanci turjiya mai ƙarfi musamman daga jihohin yankin arewacin ƙasar, waɗanda ke fargabar idan an amince da shi, zai mayar da yankin baya ta fuskar tara kuɗaɗen shiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *