Mun ɗau alwashin ceto mata da kuma ɗalibai da ƴan bindiga suka sace – Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Gwamnatin tarayya ta sha alwashin hada karfi da karfe don ganin an kuɓutar da ɗaliban makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kuriga da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna da kuma ‘yan gudun hijira a unguwar Wurge da ke karamar hukumar Ngala ta jihar Borno da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci sace mutane ba, kuma ya saɓa wa ɗabi’u na ɗan Adam.

Ya ce gwamnati tana Alla-wadai da duk wani nau’i na tashin hankali ko afka wa jama’a da ba su ji ba ba su gani ba, musamman marasa galihu.

Idris ya bayyana cewa yara sun cancanci neman ilimi a yanayin da babu cutarwa, kuma duk wata barazana da za ta iya kawo musu cikas a karatu, to barazana ce ga zaman lafiyar ƙasar.

Rashin tsaro ya ɗaiɗaita ƴan Najeriya sama da miliyan shida

Gwamnatin jahar Kano Ta Yi Alkawarin Kara Inganta Ilimin Yaya Mata Don Raba Su Da Yawon Tallace-tallace.

Yayin da yake jajantawa iyalai da kuma al’ummar da abin ya shafa, Idris ya ce shugaban Bola Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su gaggauta ganin an ceto dukkan waɗanda aka sace, tare da kamo waɗanda suka yi wannan aika-aika.

A cewarsa, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an yi wa waɗanda abin ya shafa adalci da kuma tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata laifin bisa tsari na doka.

Ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu amma su rika sa ido, sannan su bai wa jami’an tsaro bayanai da suka dace waɗanda za su taimaka musu.

“Aiki tare da haɗin kai na da matukar muhimmanci idan har muna son a yaki matsalar ‘yan fashi, ta-da kayar baya da kuma rashin tsaro a ƙasarmu yadda ya kamata.”

“Bugu da kari, gwamnati na sake jaddada kudurinta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa, kuma za ta ci gaba da yin aiki tukuru don ganin ta kawo karshen ɓata-gari,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *