Muna da fetur ɗin da zai ishi Najeriya gaba ɗaya – Dangote

Spread the love

Matatar man fetur ta Dangote ta ce tana da fetur mai yawa a lalitarta da zai ishi buƙatun Najeriya baki ɗaya, kamar yadda shugaban kamfanin Aliko Dangote ya bayyana.

Da yake magana a ƙarshen mako, Dangote ya ce matatar na da mai sama da lita miliyan 500.

Kalaman nasa na zuwa ne daidai lokacin da direbobin manyan motoci masu dakon mai ke yajin aiki a jihar Legas sakamakon abin da suka kira “cin zali” da ‘yansanda ke yi musu a titunan birnin.

“Yanzu da muke magana, muna da lita sama da rabin biliyan. Matatar na samar da albarkatu isassu kamar fetur, da dizel, da kalanzir domin amfanin ‘yan Najeriya 100 bisa 100,” in ji Dangote.

Ya faɗa wa tawagar wakilai daga ƙasar Zambia cewa “da ma matatar an yi ta ne ba don Najeriya kawai ba, an yi ta ne domin amfanin Afirka baki ɗaya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *