Anyi kira ga Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif daya kai ɗauki, ga ɗaliban da sukayi karatun Diploma a fannin shari’a da kuma aikin Lauya a Kwalejin koyar da aikin shari’a ta Kano, wato (Aminu Kano college of Islamic and Legal studies), a sakamakon yadda ake ƙoƙarin kassara karatun nasu.
Ƙungiyar dake Kare Haƙƙin Ɗan Adam, yaƙi da rashin Adalci dama bibiya akan Shugabanci na gari (War Against Injustice) ce tayi wannan kira, ta bakin babban daraktan ta Kwamared Umar Ibrahim Umar, cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR HAUSA a daren jiya, inda yace ɗaliban suna neman agajin gaggawa daga Gwamnan.
- NDLEA Ta Cafke Ma Su Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi A London Evening Kano.
- Yan Sanda Sun Zargin Wasu Mutane Da Karbar Belin Yan Dabar Da Aka cafke A Dorayi.
Hukumar Dake shirya Jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ce ta haramtawa ɗaliban da suka mallaki Diplomar Makarantar Legal ɗin shiga sahun waɗanda za’a bawa Aji Biyu a Jami’oin Ƙasar nan wato (Direct Entry).
A cewar Kwamared Umar, ” Matakin Hukumar JAMB ɗin ya janyo babbar asara dama sanya zulumi a zukatan ɗaliban da suka kammala Karatun Diplomar da waɗanda suke ciki, harma da iyayen yaran da suka ɗauki nauyin karatun yaran nasu”.
Dama wannan Diploma ita ce hanyar da talakawan jihar Kano suke samun sauƙi wajen yin karatun aikin Lauya ko kuma karatun shari’a, mafari kenan da matakin Hukumar JAMB ya zama barazana a gare su.
Adan haka ne ƙungiyar tayi kira ga Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusif, da ta kawo wa ɗaliban ɗauki, ta hanyar shiga maganar duba da yadda Hukumar ta tsaida ranar 11 ga watan Afrilun nan da muke ciki a matsayin ranar da zata rufe.
Ƙungiyar ta ce wannan rashin shiga tsakanin akan wannan magana zai matuƙar illata jihar Kano, duba da yadda mafi yawancin ‘ya ‘yan talakawa basu da damar shiga Jami’a kai tsaye har sai sun bi ta Makarantar legal.
A ƙarshe Ƙungiyar tayi fatan Gwamnatin Kano zata kawo wa ɗaliban ɗauki ta yadda zai zama suma sun sami damar morar karatun da sukayi a Makarantar Legal ɗin ne ɗumbin tarihi a kano da ma Najeriya gaba-ɗaya.
A Shekarar da ta gabata ne Hukumar Dake shirya Jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB), ta haramtawa ɗaliban Makarantar Legal shiga sahun waɗanda za’a bawa aji biyu a Jami’oin Ƙasar nan, domin su sami ragin shekara guda wajen yin karatun Digiri.