Muna fatan INEC za ta ɗauki darasi daga zaben Senegal

Spread the love

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya taya sabon zaɓaɓɓen shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye murnar lashe zaɓen ƙasar da aka yi a ranar 24 ga watan Maris ɗin 2024.

Cikin wani sakon X da ya wallafa a yammacin Juma’a, Atiku ya ce nasarar gudanar da zaɓen lafiya ƙalau, ya nuna akwai kyakkyawan fatan ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin soji su ma za su iya komawa kan tsarin dimokraɗiyya a nan gaba.

“A wajenmu Najeriya da wasu wuraren, akwai babban darasi da ya kamata mu koya a zaɓen Senegal

“Wannan yana ƙara tabbatar da cewa a ƙarƙashin dimokraɗiyya ne ake iya samar da gwamnati mai inganci,” in ji Atiku.

Ya ce abin da aka gani a zaɓukan Najeriya na 2019 da na 2023 sun nuna INEC ba ta yi abin da muka yi tsammani ba.

“Ina taya shugaban Faye murnar lashe zaɓe. Fatana shi ne zaɓen ya zama mai alfanu ga mutanen Senegal kuma ya zama zakaran gwajin dafi ga sauran ƙasashen Yammacin Afrika.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *