Muna Goyon Bayan Talaka Ya Fita Neman Haƙƙinsa – Kungiyar Makarantun Islamiyyu Da Tsangayu Ta Kano.

Spread the love
Ƙungiyar haɗin kan Makarantun Islamiyyu da Tsangayu ta jihar Kano, ta goyi bayan Zanga-zangar da talakawan ƙasar zasu fita a gobe Alhamis 1 ga watan Augusta.
Shugaban Ƙungiyar Sheikh Kamalu Sa’id Mai Jabbaru ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da manema labarai a Kano, inda ya ce tunda shugabanni sun gaza sauke haƙƙin dake kansu toh lallai subar talaka ya tashi ya nemi haƙƙinsa da kansa.
A cewar “Takanas Malamai suka je wurin Shugaban Ƙasa suka gaya masa halin da talaka yake ciki amma yayi burus, kuma makusantansa sunƙi gaya masa gaskiya domin ya ɗauki mataki tun kafin lokaci ya ƙure masa”.
Bugu da ƙari ya bayyana yadda wasu jihohin Arewacin ƙasar suke cikin halin rashin tsaro, ta yadda ake garkuwa dasu domin neman kuɗin fansa koma cin zarafinsu a mafi yawancin lokuta.
Toh sai dai kuma yaja hankalin masu yin zanga-zangar da su gudanar da ita cikin nutsuwa ta hanyar bin doka da oda, harma yayi fatan Jami’an tsaro zasu kiyaye take haƙƙoƙin masu neman haƙƙin nasu.
A ƙarshe yayi fatan Allah ya kawo wa talakawan ƙasar mafita, akan wannan hali da suke ciki na Talauci dama ƙuncin rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *