Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya ce akwai batutuwa da dama da yake so a duba yayin taro a birnin Tel Aviv, a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza.
Mista Blinken yayin wata ganawa da shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya jaddada muhimmancin rage hare-haren da suke jikkata fararen hula a Gaza.
Ya ƙara neman Isra’ilar ta samar da kafar shigar da kayan agaji.
Wasu manyan wakilan ƙasashen Turai dai sun ce, ƙulla yarjejeniya a tsakanin yankuna gabaɗaya, ita ce hanyar samar da mafita a rikicin.
Mista Blinken zai gana da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu tare da mukarraban gwamnatinsa, kafin ganawarsa da iyalan wasu daga cikin ‘yan Isra’ila da aka yi garkuwa da su a Gaza, dangane da hanyoyin da za a bi wajen ganin an sako su.