Gamayyar kungiyoyin farar hula a Najeriya sun yi kiran a tattauna domin jawo hankalin Mali da Nijar da Burkina Faso su zauna a kungiyar Ecowas kasancewar ficewarsu zai jawo cikas a yakin da ake da ta’addanci a yankin.
Kasashen uku na yankin Sahel da ke karkashin mulkin sojoji sun sanar da kudurinsu na ficewa daga Ecowas ranar 28 ga watan Janairu inda suka ce “kungiyar ta zama barazana ga mambobinta”.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa gamayyar kungiyoyin ta bukaci a samar da matakai na hana rabewar kamar yadda ta sanar cikin wata sanarwa.
‘Kaso 30 na mace-macen Jarirai a Duniya na faruwa ne a Najeriya
“Ficewar nakasu ne ga burin samar da hadin kan tattalin arziki a Ecowas har da samar da tsarin kasuwanci maras shinge tsakanin kasashe mambobin kungiyar. Zai yi mummunan tasiri ga rayuwar mutanen Afirka ta Yamma,” in ji kungiyoyin.
Gwamnatin Najeriya ta soki kasashen uku saboda ficewa daga kungiyar inda ta ce sojojin sun dauki matakin ne domin burge jama’a.
Yankin Afira ta Yamma na fama da matsalar tsaro da juyin mulki a wasu kasashe kuma rarrabuwar kan kungiyar Ecowas na iya tabarbara yanayin da galibin kasashen yankin ke ciki.