Amadadin daukacin Al’ummar Kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure da Mutanen Kano ta Kudu da Jihar Kano baki daya, Ni FATIHU YUSUF BICHI (Maimagana da yawun RT Hon Kabiru Alhassan Rurum) nake Mika sakon Jinjina da godiya ga Alh Auwalu Abdullahi A.A Rano bisa yadda ya bada katafariyar makaranta da yake ginawa a garin Rano kyauta yace aje a maida ita Federal Polytechnic da Shugaban Kasa ya Amince ayi a garin.
A.A Rano ya cewa Rt Hon Rurum ” KABIRU AJE A DUBA BABBAR MAKARANTAR NAN DA NAKE GINAWA A RANO IN ZATAYI NA BATA ITA KYAUTA GA GWAMNATI A CIGABA DA AIKIN MAIDA ITA FEDERAL POLYTECHNIC DAKA NEMO IN KUMA BAZATA ISA BA TO A NEMO FILI A KO INA NI ZAN SIYA KO NAWA NE IN BAYAR AYI WANNAN AIKI NA CIGABAN GARINMU”..Inji A.A Rano.
RT Hon Kabiru Alhassan Rurum ya Umarci in Mika sakon godiyarsa ta musamman ga AA Rano bisa yadda yake nuna kishin Jama’a da taimakonsu da bada gudummuwa a duk lokacin da wani Abu na cigaba ya taso ko a rano ko Kibiya ko Bunkure ko a yankin Kano ta Kudu.
Da fatan Allah ya kara bunkasa Arzikinka ya Kuma kiyaye dukiyarka yasa ka gama lafiya Amin…
Haka Kuma daukacin Matasan Gidan Siyasar RURUM da masoyansa na tayaka murnar samun girmamawa da aka baka a Jami’ar Bayero dake Kano a Yau da fatan Allah ya Karo ninkin ba ninki….
Fatihu Yusuf Bichi
Senior Special Assistant to Rt Hon Kabiru Alhassan on Media and Publicity.
Feb 15, 2025