Munfi Samun Bayanai Daga Bangaren Mata: Rundunar Yan Sandan Kano

Spread the love
SP Abdullahi Haruna Kiyawa Kakakin Yan sandan Kano

Rundunar Yan Sandan Jahar Kano ta bayyana cewa Iyaye Mata, sun zarce Maza Wajen ba su bayanan abubuwan da suke faruwa a sassan Jahar Kano, don kawo daukin gaggawa na dakike aiyukan batagari.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan ta cikin shirin Dan Sanda Abokin Kowa na Freedom Radio, a Ranar Lahadi.

SP Abdullahi Kiyawa, ya ce, matan suna sanar da sune ta Hanyar lambobin wayar da suke bayarwa a koda yaushe, ne ya kawo wannan Ci gaban.

Sai dai ya Kara yin Kira ga sauran al’umma, su ci gaba da bayar da goyon baya ga hukumomin tsaro, domin aikin tsaro ba na dan sanda kadai ba ne harda sauran al’umma.

A cewarsa lokaci yanayin tarbiya ya Kara lalacewa, sakamakon sakacin wasu iyaye akan yayansu, na rashin bibiyar wadanda suke mu’amulla da su , inda suke fada wa harkar shan miyagun kwayoyi, kwace da harkar Daba.

Kakakin Yan sandan Jahar Kano ya Kara da cewa , an samu babbar nasarar dakile harkar Fashin waya da aiyukan Daba, sakamakon hadin Kai da kuma addu’o’in da al’ummar Jahar ke Yi akoda yaushe.

Tuni dai wasu rahotanni ke bayyana cewa, wasu daga cikin Matasan da suka addabi, yankin Unguwar Dorayi da aiyukan Daba, sun bayar Jahar, sakamakon cafke wasu da jami’an tsaro suka Yi da kuma Kara fadada sintiri a yankin.

Ka makon da gabata sai rundunar Yan sandan Jahar Kano, ta cafke matasa 104 , sannan ta gurfanar da su a gaban kotu, bisa zarginsu da aiyukan Daba da kuma Ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Wannan nasarar ta samu ne sakamakon fito da dabarun magance matsalar da Kwamishinan Yan sandan Jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya yi a fadin Jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *