Musa Iliyasu Kwankwaso ya kama aiki a mukamin da Tinubu ya bashi

Spread the love

Tsohon kwamishinan ma’aikatar raya karkara ta jihar kano Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya karɓi takardar kama aiki a matsayin mamba na hukumar gudanar da Kwalejin ilimi ta tarayya dake Okene a jihar kogi .

Idan za’a iya tunawa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ne ya nada Musa Iliyasu Kwankwaso da wasu yan Nigeria a matsayin shugabanni da mambobin hukumomin gudanarwa na jami’o’in da kwale ilimi na tarayya.

Lokaci da ya karɓi takardar kama aikin Musa Iliyasu Kwankwaso ya ba da tabbacin zai yi amfani da dimbin kwarewar da yake da ita wajen ciyar da Kwalejin gaba.

Bayan karbar takardar kama aikin Musa Iliyasu ya kaiwa shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje domin ya sa masa albarka tare da yi masa godiya bisa gudunnawar da ya bayar har ya sami mukamin a matsayin sa na jagoransu a siyasan ce.

Dr. Ganduje ya taya Musa Iliyasu Kwankwaso da sauran wadanda suka sami mukamin daga jihar kano murnar samun wannan mukamin.

Sai dai ya ja hankalin su da su mai da hankali wajen sauke nauyin da shugaban kasa Bola Tinubu ya dora musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *