Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar lll, ya ce musulunci ba ya hana yara mata karatu.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a jihar Bauchi a wajen taron shirin inganta ilimin mata na AGILE, wanda ma’aikatar ilimi ta jihar Bauchi ta haɗa tare da babban bankin duniya.
An yi taron ne a ƙarƙashin taken: “kawo ƙarshen abubuwan da suke hana mata zuwa makaranta a arewa maso gabas: Rawar da sarakunan gargajiya da malaman addini za su taka.”
Sarkin Musulmin ya ce, “Musulunci ba ya hana yara mata neman ilimi. Akwai wasu abubuwan da suke kawo musu tsaiko wajen neman ilimi. Da nake hanyata ta zuwa nan, na ga ƙananan yara suna talla a titi. Da na tambaye su, sai suka faɗa min cewa akwai makarantar safe da ta yamma.
“Karatun yara mata na da muhimmanci saboda su ne za su ilimantar da iyalinsu da al’umma,” in ji shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A ƙarshe ya yi kira ga gwamnonin arewa su ƙara zuba kuɗaɗe a ɓangaren ilimi domin ilimantar da yara mata da maza na yankin.