Mutane 14 Sun Rasu A Wani Mummunan Hatsarin Mota A Jigawa

Spread the love

Wani mummunan hatsarin mota ya Yi sanadiyar rasa rayukan mutane 14 , sannan wasu hudu kuma Suka samu raunika a garin Kanya Babba a jahar Jigawa.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa, hatsarin ya faru ne a garin Kanya Babba da misalin karfe 11:30am na safiyar Ranar Talata, tsakanin Wata motar DAF da kuma Hiace lokacin da mai motar yake kokarin kauce wa Jami’an hukumar shige da fice , wadanda Suka tsayar da shi , inda Suka Yi taho mugama da DAF ,din har mutane 14 Suka rasu.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Jigawa DSP Shiisu Lawan Adamu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Saurari sautin muryar Kakakin rundunar yan sandan jahar Jigawa DSP SHIISU LAWAN ADAMU

 

Ya ce bayan faruwar lamarin Baturen yan sandan Kanya Babba, da yaransa  sun garzaya wajen tare da dibar mutanen tare da Kai su asibiti, inda ya tabbatar da rasuwar mutane 14 ya yin da sauran hudu kuma suke samun kulawar gaggawa.

Wadanda Suka rasa rayukan su , sun hada da Rabi’u Isah, Babangida Mai Hura , Naziru Habibu, Ado Sallau, Yusuf Muhammed, Hassana Yan Biyu , Na’ima Magaji da kuma Ado Bawa.

Sauran su ne , Dan Nai’ma, Alhaji Ami , Nuhu Dahir, Mallam Abdu, Dasoto da kuma Yaron Motar da ba a bayyana Suna sa ba.

DSP Shiisu Lawan , ya Kara da cewa, yanzu haka an kaddamar da bincike domin gano musabbabin faruwar hatsarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *