Mutane 17 Ne Suka Rasu Sanadiyar Kunna Mu Su Wutar Fetur: Yan Sandan Kano

Spread the love
SP Abdullahi Haruna Kiyawa Kakakin Yan sandan Kano

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta tabbatar da mutuwar mutane 17 cikin 24 da suke kwance a Asibitin Murtala Muhammed, sakamakon kunna mu su wutar Fetur , da ake zargin wani matashi mai suna Shafi’u Abubakar, kan ricikin gado.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Ranar Lahadi.

Idan ba a manta ba jaridar, Idongari.ng, ta ruwaito mu Ku cewa, lamarin ya faru ne a Ranar Laraba 15 ga watan Mayu 2024, a yankin Gadan dake Karamar hukumar Gezawa Kano.

Abaya dai rundunar yan sandan jahar Kano, ta ce sun samu kiraye-kirayen jama’a kan cewar wuta ta tashi da misalin karfe 5:20am na Asuba, a wani masallaci dake kauyen Gadan Karamar hukumar Gezawa, a daidai lokacin da suke yin sallar Asuba, wadanda mutane da dama Suka samu ranuka.

Bayan samun rahotan ne Kwamishinan Yan Sandan Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya tura wasu jami’an yan sanda , wadanda Suka kware kan duk wani Abu da yake tashi kamar Abun fashewa da dai sauransu, karkashin jagorancin CSP Haruna Isma’il, da kuma Baturen yan sanda na Gezawa CSP Haruna Iliya, tare da ba su umarnin a gaggauta zuwa wajen da lamarin ya faru, dan ganin an yi abunda yakamata.

SP Abdullahi Kiyawa, ya Kara da cewa, bayan sunje wajen ne , aka samu nasarar toshe ko’ina ,tare da gaggauta ceto mutane 24, inda aka garzaya da su Babban asibitin Murtala Muhammed, a Birnin Kano.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kara da cewa mutane 24, da aka kwantar a asibitin Murtala Muhammed, yanzu haka 17 sun mutu.

Binciken yan sanda na farko-farko, ya tabbatar da cewar, an jefa wuta ne ta Hanyar amfani da man Fetur.

Kakakin yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce yanzu haka Wanda ake zargi na farko mai suna Shafi’u Abubakar, an Kama shi, kuma ya tabbatar da cewa shi ne yaje ya siyo man Fetur a gidan mai, sannan ya sanya a cikin Wata roba ya watsa a cikin masallacin ya kunna wuta.

Rahotanni sun bayyana cewa, hakan ya faru ne sakamakon rigimar cikin gida ta rabon gado, kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za a Gurfanar da shia gaban kotu don ya fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *