Mutane 22 Sun Fada Komar Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa Bisa Zargin Aikata Laifuka Maban-banta

Spread the love

 

Rundunar Yan Sandan jahar Jigawa, karkashin jagorancin kwamishinan ta , CP A.T. Abdullahi, ta samu nasarar kama wadanda ake Zargi da Lalata kadarorin gwamnati musamman Wayar wutar lantarki a kananan hukumomin, Kafin Hausa, Malam Madori, Yankwashi da kuma Sule Tankarkar.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Jigawa DSP Shisu Lawan Adamu, ne ya bayyana hakan ga idongari.ng , ta cikin wata sanarwa da ya aike mata a ranar Asabar.

Sanarwar ta kara da cewa an cafke wasu da ake Zargi da satar Shanu, a kananan hukumomin Kafin Hausa, Malam Madori, Kirikasamma da kuma Ringim dake jahar.

Haka zalika Rundunar ta yi nasarar kama ma su zambatar jama’a, a kananan hukumomin Dutse da kuma Kiyawa, tare da tarwatsa wadanda ake Zargi da aikata laifin sata lokacin da mutane suke bacci a kananan hukumomin, Kazaure da kuma Taura.

Idongari.ng , ta ruwaito cewa an kama wasu da ake Zargi da aikata laifukan Fashi da makami, a karamar hukumar Malam Madori, a lokacin da suka shiga gidajen mutane da muggan makamai, domin su yi mu su Fashi.

Rundunar Yan Sandan jahar Jigawan ta sake kama wadanda ake Zargi da yin algus ta hanyar jirkita takin zamani su Sanya masa wasu Abubuwa sanan su siyar wa da al’umma don ya Yi auki.

Kazalika an kama wadanda suke ta’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jahar.

Saurari muryar kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Jigawa DSP Shisu Lawan Adamu

Wannan dai na.zuwa ne bayan wani sumame da dakarun Rundunar Yan Sandan ta Kai a sassa daban-daban na jahar, Inda aka kama mutane 22.

Cikin kayayyakin da Yan Sandan suka kwato sun hada da motacin da ake Zargi ana satar Shanu da su, Babura 3 , Shanu 6 da kuma Takaddar rubutu A4 reams 50 bayan an damfari Mai kayan ta hanyar Tura masa Alert na bogi.

Sannan an samu kudi sama da naira Dubu hasim da tara, da Dalar Amurika ta Jabu tare da wayoyin lantarkin da aka lalata harma da miyagun kwayoyi.

Kwamishinan yan Sandan jahar CP A.T. Abdullahi, ya Yi kira ga al’umma musaman Yan Kasuwar da suke amfani da Dalar Amurika ,su kasance ma su Sanya Ido akoda yaushe don kaucewa fada wa Hannun Yan Damfara.

A karshe Rundunar ta ja hankalin al’umma su daina daukar doka a hannunsu , idan an samu wani da ake Zargi da aikata laifi , su dinga damkashi a Hannun hukumomin tsaro don daukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *