Aƙalla mutum shida ne suka mutu bayan kifewar amalanke a cikin wani rafi da ke yankin Gantsa na jihar Jigawa.
Jam’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Buji, Ali Safiyyanu ya tabbatar wa BBC da afkuwar lamarin.
Ya ce bayan an gama aikin ceto ne da kuma fitar da waɗanda suka faɗa cikin ruwan ne aka garzaya da su babban asibitin Gantsa inda aka tabbatar da mutuwar mutanen.
Ya ƙara da cewa adadin mutanen da suka faɗa cikin ruwa sun kai mutum 10 inda tuni aka sallami huɗu yayin da kuma matuƙin amalanken ke ci gaba da karɓar magani a asibiti.
Ya kuma ce cikin waɗanda suka rasu, har da yara biyu da suka ƙwace daga hannun iyayensu.
“Mutanen sun faɗa cikin ruwan ne sakamakon karyewar amalanke.”
“Tun bayan da ruwa ya cinye hanyar da mutane ke bi ne ake amfani da amalanke da kwale-kwale wajen tsallakawa”.
“Ana tsallakawa da su ne daga Gantsa zuwa wani ruwa da ake tsallakawa domin a hau mota a tafi Sara inda akwai wata kasuwa da ke ci a duk ranar Talata.”
“Mutanen na cikin ruwan ne lokacin da sandar amalanke ta karye, saboda haka wasu suka tsorata inda suka yi yunƙurin fita sai kuma amalanken ya juye da su.” in ji jami’in
Ruwan sama mai yawa da ake samu a yankunan Najeriya ya sanya an samu ambaliya a sassa da dama, lamarin da ya haifar da katsewar hanyoyin sufuri sanadiyyar ɓallewar gadoji.
Ya zuwa yanzu Hukumar kai agajin gaggawa ta Najeriya ta tabbatar cewa aƙalla mutum 49 ne suka rasa rayukansu a fadin ƙasar.