Mutane 6 sun rasu daga cikin 14 da wani ginin Bene ya danne a Kano

Spread the love

Wani ginin Bene mai hawa ɗaya da ake ginawa a unguwar Kuntau kusa da layin Uba Safiyanu, da ya ruguzowa mutane sama da 13, an yi zargin ya yi sanadiyyar rasuwar mutane shida, ciki kuwa har da mai gidan da kuma mai aikin ginin.

Ginin benen dai mai hawa ɗayan ya ruguzo ne a wannan rana ta Juma’a, a dai-dai lokacin da wasu mutane da dama suka fakewa ruwa a jikin gidan, al’amarin da ya danne akalla mutane sama da 13, wanda ya yi sanadiyyar mutane da dama.

Dagacin Dorayi Babba Mallam Musa Badamasi, ya shaida wa Dala FM, cewa, a gaban sa an zaƙulo aƙalla mutane 12 daga cikin baraguzan ginin, inda tuni mamallakin gidan da kuma mai aikin gidan suka rasu, inda aka kai su Asibiti.
Dagacin ya kuma shawarci al’umma da su rinƙa neman shawarwarin masana
aikin Gini, a duk lokacin da za suyi gini, ta yadda za’a kaucewa fuskantar matsala irin wacce aka samu.

Yanzu haka dai ana ci gaba da fargaba yayin da ake ci gaba da bada agajin gaggawa a wajen, domin tonon sauran wadanda ginin ya danne.

Idan dai ba’a manta ba ko a kwanakin baya, sai da aka samu ruguzowar
wani ginin Bene a unguwar ta Kuntau al’amarin da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama, inda ko a ranar Alhamis, ma sai da aka samu ruguzowar wani ginin Bene mai hawa uku da ake ginawa a unguwar Sharada kwanar kasuwa, amma bai danne kowa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *