Mutane 7 Sun Mutu 11 Sun Jikkata A Hadarin Mota A Niger.

Spread the love

Mutane 7 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu goma sha daya suka samu munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a unguwar Essa dake kan titin Agaie Badeggi a karamar hukumar Katcha a jihar Neja.

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, NSEMA Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar hatsarin a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Minna.

A cewar Abdullahi Baba Arah, motar na dauke da hatsin gwamnatin tarayya, da kuma wata mota dake dauke da wasu fasinjoji 36, wadanda dukkansu maza ne zasu jihar Kano daga jihar Legas suka yi toho mu gama a lokacin da hatsarin ya afku.

Hatsarin ya afku ne da misalin karfe uku na safiyar yau, sakamakon rashin kyawun hanya a layin Lambata, Bida.

Ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, an tabbatar da mutuwar mutane 7,  11 da suka samu munanan raunuka, yayin da mutane 5 suka samu kananan yara.

Wasu daga cikin wadanda suka jikkata an kai su cibiyoyin lafiya na Badeggi da Agaie, wasu kuma abokan aikinsu sun tafi da su yayin da ‘yan uwansu kuma suka tafi da wadanda suka mutu domin yi musu jana’iza.

A halin da ake ciki dai hukumar NSEMA ta gudanar da aikin bincike da ceto tare da matafiya da wasu mutanen kauyen da ke kusa da inda lamarin ya faru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *