Wani mummunan Hatsarin Mota ya da Faru a babbar Kasuwar Kura dake jahar Kano , ya Yi sanadiyar rasa rayukan mutane 8, sannan wasu da dama suka jikkata.
Shaidun gani da Ido sun Tabbatar wa idongari.ng cewa babbar motar danne Baburin Adaidaita Sahu , kuma dukkan wadanda suke cikin Baburin nan ta ke suka rasu.
- DSS Ta Sako Ajaero Kafin Cikar Wa’adin NLC
- Yan Sandan Kano Sun Kubutar Da Yaron Da Aka Yi Garkuwa Da Shi Tare Da Kama Wadanda Ake Zargin
Jamilu Kura ya ce motoci ne na kamfani wadanda suka biyo kan titin zuwa Zaria , inda daya daga ciki motar ta fara ture wata Mai masara da kuma wasu mutane da suke cikin Baburin Adaidaita Sahu bayan sun dawo daga Gona.
Tuni dai wasu fusatattun matasa suka Kunnawa motar Wuta, Inda jami’an Yan sanda da jami’an bijilanti suka taimaka don kwantar da hankulan al’ummar yankin.
Mutanen da suka rasu da kuma Wadanda suka jikkata tuni aka garzaya da su babban asibitin karamar hukumar Kura.
Ko a makon da gabata sai da aka samu iftila’in hatsarin mota, har ta yi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama yayin da wasu kuma suka jikkata bayan sun iddar da sallah juma’a.