Hatsarin mota ya yi ajalin mutane 9, wasu uku sun jikkata a wani hatsarin mota a yankin Kira da ke Jihar Kano.
Hatsarin ya auku ne a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kano a ranar Laraba.
Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar aukuwar hatsarin a tsakanin wata babbar mota da babur mai kafa uku.
Kakakin hukumar, Abdullahi Labaran ya bayyana cewa, “mutum tara sun riga mu gidan gaskiya, wasu uku sun samu raunuka.”
Ya ce an kai wadanda suka ji raunin Babban Asibitin Kura, inda ake ba su kulawa.
Jami’in ya bayyana cewa, binciken farko ya nuna motar ta kwace ne a sakamakon kokarin yin ‘overtaking’ ba daidai ba.
Daga nan ya bukaci masu ababen hawa su kiyaye dokokin hanya su guji tukin ganganci da gudun wuce ka’ida.
- Sojoji sun hana yunƙurin ‘ƴan ta’adda’ na kai hari kan kadarorin DSS a Neja
- Kano ta sanar da sabuwar ranar komawa makarantu a jihar