Rundunar yan jahar Jigawa ta tabbatar da Rasuwar mutane 94 , ya yin da 50 da aka kwantar da su a asibitin Ringim, Sakamakon faduwar Tankar mai , a Garin Majia dake karamar hukumar Taura ta jahar.
Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Jigawa, DSP Shisu Lawan Adamu, ya tabbatar da faruwar lamarin, Inda ya ce abun ya Faru ne da misalin karfe 11:30pm na daren jiya Talata.
Ya kara da cewa hakan ya Faru ne sakamakon malalar da man Fetur din yake Yi cikin magudanan ruwa, Inda su kuma mutanen Garin suka fito suna diba , hara wuta kama wuraren da man ya malale.
Idongari.ng , ta ruwaito cewa bayan faruwar lamarin jami’an Yan Sanda da kuma na hukumar kashe Gobara, sun Kai daukin gaggawa inda suka kwashe mutanen zuwa asibiti tare da kashe Gobarar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Direban Tankar , Yusuf Mohd Hotoro, Dan asalin jahar Kano, ya taso daga Kanon da zummar zuwa Garin Guru, Inda ya kasa sarrafa motar har ta fadi a kusa da jami’ar Khadija , a jahar Jigawa.
Kwamishinan Yan Sandan jahar Jigawa CP A.T. Abdullahi, ya jajanta wa al’ummar jahar Jigawa, bisa iftila’in da ya Faru.
A karshe Rundunar ta gargadi jama’a da su kaucewa jefa kansu cikin hadari a duk lokacin da hakan ta Faru sakamakon son dibar banza har su Kai kaisu ga halaka.