Fadar shugaban Najeriya ta ce shugaba Tinubu ya yi garambawul game da ayyukan jami’ansa da ya naɗa a sashen hulɗa da kafafen yaɗa labaru, domin bunƙasa ɓangaren.
Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa labaru da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar ta ce a yanzu dukkanin mutane uku da aka naɗa a muƙaman yaɗa labaru za su zamo masu magana da yawun shugaban ƙasa.
Sai dai sanarwar ta ce Mista Sunday Dare a yanzu shi ne mai bai wa shugaban ƙasar shawara na musamman kan kafafen yaɗa labaru da hulɗa da jama’a.
Haka nan Mista Daniel Bwala, wanda a makon da ya gabata aka bayyana a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan kafafaen yaɗa labaru da sadarwa yanzu zai riƙe muƙamin mai bayar da shawara na musamman kan yaɗa manufofin gwamnati.
Sanarwar ta ce idan aka yi la’akari da cewa akwai kuma Bayo Onanuga, wanda shi ne mai taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa dabarun gwamnati “za a ga cewa babu mutum ɗaya tilo da ke riƙe da muƙamin mai magana da yawun shugaban ƙasa”.
“Saboda haka dukkanin mashawartan na musamman uku za su zamo masu magana da yawun gwamnati.”
An dade dai ana raɗe-radin cewa akwai rashin jituwa a ɓangaren masu taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa labaru, inda ayyukan wasu jami’an ke shiga cikin na wasu.
A cikin watan Satumban da ya gabata ne, mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Nagelale ya ajiye muƙaminsa ‘bisa wasu dalilai na ƙashin kai’ kamar yadda ya bayyana.
Sai dai kafafen yaɗa labaru da dama sun yi bayanin cewa ajiye muƙamin nasa ba zai rasa nasaba da rashin jituwar da ke tsakanin jami’an da shugaba Tinubu ya naɗa a ɓangaren yaɗa labarun na fadar shugaban ƙasa ba.