Mutanen Danzaki Sun Koka Kan Wani Aiki Da Ya Biyo Ta Cikin Gonakinsu, Makabarta Da Makaranta

Spread the love

Asafiyar wannan rana mutanen yankin Danzaki suka wayi gari da an wani kamfanin aikin hanya yace zaiyi aikin wata hanya da zata tafi har zuwa Garin Dawanau dake cikin k

Al’ummar Garin ‘Danzaki dake cikin karamar hukumar Gezawa sunyi kira ga mai girma Zababben Gwamnan kano Injiniya ABBA KABIR YUSUF da ya kawo musu dauki akan wani aiki da ya biyo ta cikin Makabarta, makaranta da kuma Gonakin jama’ar garin na ‘Danzaki.

Inda suka ce, da farko an fitar da inda za’ayi aikin a gurin da bai shafi gidajen Talakawan gari ko Gonakin su ba, daga bisani sai suka samu labarin akwai wani mai farcen susa ‘Dan wani tsohon shugaban kasa, wani lokaci da ya gabata, wanda yayi uwa da makarbiya aka mayar da aikin cikin Makabarta, makaranta da kuma gidajen jama’ar yankin kamar yanda Alhaji Lawan wanda ya jagoranci mutanen garin ke shaidawa wakilin mu da ya ziyarci Garin daidai lokacin da abin ya faru.

 

Yana mai cewar, mutanen garin masu bin doka da oda ne, kuma masu biyayya ga magabata ne musamman gwamnati.

A don haka yace, a baya an baiwa wasu mamallaka gidaje da Gonaki katin da zasu Karbi diyyar guraren su da akace aiki ya biyo ta kansu, amma har yanzu ba’a biya mutanen ba.

Kwatsam rana tsaka akace an sauya inda za’ayi aikin zuwa cikin Makabarta, makaranta, Gonaki da kuma gidajen jama’ar garin na Danzaki.

Jin hakan ne tasa muka tuntubi mai unguwar ‘Dan Kargo Malam Amadu Ibrahim ‘Danzaki a karamar hukumar Gezawa, inda ya tabbatar da faruwar lamarin, amma shima ya sake jaddada rokon sa ga mai girma Gwamnan kano akan wannan lamarin da suke zargin ba zai haifar da ida mai Ido ba.

Ya kara da cewar, yanzu haka mutanen garin basa iya yin Bacci, basu da Nutsuwa da kwanciyar hankali sakamakon jin za’a karbe musu gidaje da Gonakin jama’ar garin.

A karshe ya roki Gwamnan kano da masu ruwa da tsaki akan wannan lamarin su dubi halin da mutanen garin ke ciki, su tausaya musu.

Shugaban karamar hukumar Gezawa Alhaji Bala Mukaddas ta bakin kansilan mazabar Jogana Hon Arma ya’u Muhammad Danzaki yace, har yanzu karamar hukumar Gezawa bata samu labarin yin wannan aikin ba.

A don haka yace, basa goyon bayan yin wannan aikin a wajen da aka dawo dashi saboda wani mutum daya, gwara a mayar dashi inda aka auna za’ayi tunda farko a cewar sa.

A karshe dai wasu da kawo yanzu bamu fayyace sunan su ba, amma mun hango motar ma’aikatar kasa da safayo ta jihar kano, sun ziyarci inda za’ayi aikin sun hakur – kurtar da mutanen garin tare da yin Alkawarin zasu mika koken su ga Inda ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *