Mutanen Garuruwan Guringawa, Sheka, Shagari Kwatas Sun Nemi Daukin Mahukunta Kan Lalacewar Hanya

Spread the love

Al’ummar garin Guringawa da Sheka, Medile da Shagari Kwatas a karamar hukumar Kumbotso, sun koka kan lalacewar hanyarsu, inda hakan ya zame su tashin hankali da koma bayan yankin.

Al’ummar dai sun fito tare da yin dafifi, mazan su da mata har suke rokon gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya dube su da idon tausayin da ya saba ya kawo musu ɗauki.

Wasu daga cikin mata a yankin sun bayyana cewa rashin ya sanya ko masu ababen hawa sun dena bin hanyar Guringawa zuwa Sheka, saboda kwazazzabai da kuma zaizayar kasa da addabe su.

Haka zalika wasu maza sunce, akoda yaushe mafarkinsu na ci gaban ƴaƴansu ne da sauran al’umma, kuma sun shafe sama da shekaru 45 suna neman aikin hanyar amma har yanzu baa share musu hawaye ba.

Alhaji Ghali Sulaiman, shi ne dagacin Guringawa, ya ce a matsayin shugabannin al’umma sun yi duk abinda Yakamata wajen neman gyaran hanyar, bisa zaizayar kasar da take kara yi musu barazana.

Kano: NNPP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Ghari/Tsanyawa

Sarkin Zuru Muhammadu Sami ya rasu yana da shekara 81

  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *