Mutanen Rano,Kibiya, Bunkure Za Su Amfana Da Tallafin Kudi Na Fiye Da 45m Daga RT Hon Kabiru Alhassan Rurum

Spread the love

Daruruwan Mutane a yankin Kananan Hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure za su ji Alert Mai nauyi a gobe Litinan da Jibi talata daga Wakilin Kananan Hukumomin wato RT Hon Kabiru Alhassan Rurum

Wata Sanarwa da maimagana da yawun Turakin Fatihu Yusuf Bichi ya fitar a Yau Lahadi tace tuni Babban Darakta Yakin Neman zaben Rurum din wato Alh Alhassan Abubakar Kibiya ya Jagoranci kaddamar da tura Kudin ga wasu mutane daidai ku da Kuma kungiyoyin cigaban Al’ummar Yankin.

Kudaden da za’a turawa Mutane Sun kama daga naira dubu 100 da masu dubu 200 da masu dubu 250 har zuwa masu naira miliyan guda..

Wannan na cikin irin kokarin da *Turakin Ranon* yakeyi na ganin ya ragewa Mutanen yankin radadin matsi da halin Rayuwa da ake ciki.

*Jimillar Kudin da za’a rabar cikin kwanaki biyun a turawa Mutane ta asusun bankinsu yakai naira miliyan 45 da doriya.*

*Fatihu Yusuf Bichi*
*Media Aide to Rurum*
*21/4/2024*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *