Aƙalla mutum huɗu ne suka rasa rayukansu yayin rikicin ƙungiyoyin asiri a yankin North Bank, da ke unguwar Makurdi a Jihar Benuwe.
Wata majiya daga yankin, ta bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka yi artabu da juna, wanda ya kai ga asarar rayukan mutum huɗu cikin mako ɗaya.
A ranar Talata ne, aka ƙone wani gida a yayin da rikicin tsakanin ƙungiyoyin asirin da ya tsananta.
Mazauna yankin sun ce ƙungiyoyin biyu da aka fi sani da “Black” da “Red” sun mayar da yankin North Bank tamkar filin yaƙi, wanda ya sa jama’a suka ƙaurace wa yankin.
“Gwamnati ta ɗauki mataki yanzu, ko kuma waɗannan ƙungiyoyin za su ci gaba da kashe mutane.
“Wani ya sake rasa ransa a ranar Litinin kuma ko yau sai da muka ji harbe-harben bindiga da rana,” in ji wani mazaunin yankin.
Mazaunin ya ƙara da cewa ana shirye-shiryen birne mamacin da ya rasu a ranar Litinin.
A cewarsa ƙungiyoyin sun fara kai hari kan mai uwa da wabi.
- PERSONNEL WELFARE: CP SALMAN DOGO GARBA DECORATES 154 TRAFFIC WARDEN WITH NEW RANK
- Babban layin lantarkin Nijeriya ya sake daukewa
Shugaban wata ƙungiyar sa-kai mai suna Operation Shara a yankin North Bank, Nura Umar, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa kisan na baya-bayan nan ya faru ne misalin ƙarfe 9 na daren ranar Litinin.
Ya ce dukkannin mutanen da aka kashe matasa ne, kuma wasu daga cikinsu an yi musu kisan-gilla, inda aka sarewa wani kai.
“Lamarin yana da ban tsoro,” in ji Umar.
“Sun kashe mutum ɗaya a ranar Litinin ta hanyar harbinsa a ido. A makon da ya gabata an kashe wasu mutane uku.”
Jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Benuwe, SP Catherine Anene, ya ci tura domin ba ta amsa wayarta ba.