Wani hatsarin mota a karamar hukumar Agaie na jihar Neja ya janyo mutuwar wasu mutum huɗu.
Lamarin wanda ya afku kan hanyar Agaie zuwa Lapai, ya jikkata mutane 13.
Wata sanarwa da darekta-janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (NSEMA) Abdullahi Baba-Arah ya fitar, ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon garuwa da wasu tireloli uku suka yi da juna, inda ɗaya daga cikinsu ke ɗauke dabbobi.
“Hatsarin ya yi muni, nan take mutum biyu suka mutu yayin da sauran biyu kuma suka cika a asibiti,” in ji Abdullahi.
Jami’in hukumar ta ba da agajin gaggawa a jihar ya ce tuni aka garzaya da waɗana suka jikata zuwa babban asibitin Agaie kuma suna cigaba da karɓar magani.
Ya ce ba ya ga asarar rayuka – lamarin ya kuma rutsa da shanu 15 da akuyoyi sama da 20.