N-power : Taurin Bashi Ya Sanya Matasa Za Su Gudanar Da Zanga-zangar Kwanaki 5.

Spread the love

 

Kungiyar matasan da suka ci gajiyar shirin N-power, sun bayyana cewa har yanzu ba su cimma matsaya da gwamnatin tarayya ba, amma dai suna ci gaba da tattaunawa a shirye-shiryen da suke yi na gudanar da zanga-zangar lumana, kan basukan da suke bin gwamnatin.

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Muhammed Abubakar Habib (GMB) , ne ya tabbatar da hakan ga jaridar www.idongari.ng, ta wayar tarho a ranar Asabar.

Ya ce kamar yadda suka shirya fara gudanar da zanga-zangar daga ranar Litinin 2 zuwa 6 ga watan Disamban 2024 tanan daram sakamakon har yanzu ba su cimma matsaya ba, inda za su ziryaci Majalisar dokoki ta Tarayya, ma’aikatar jin kai da walwala da kuma ofishin kungiyar yan jaridu ta kasa NUJ.

 

 

Kwamared Habib, ya kara da cewa sun yi magana da ministan jin kai, Dr Nentawe Yilwatda, da kuma wasu yan majalissun wakilai, da suka shiga tsakani don ganin gwamnatin tarayyar ta biya su hakkokinsu na tsawon watanni takwas.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ne ya fito da Shirin N-power, a shekarar 2016 don tallafawa matasa wajen samun abunda dogaro da kai, sai dai an samu kalubale na rashin biyan wasu daga cikin matasan hakkokinsu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *