Na Kai Dan Uwana Asibiti Bayan Daure Shi Shekaru 10: Abdussalam Dandukulle

Spread the love

 

Mutuminan mai suna ,Abdussalam Dandukulle, mazaunin garin Wailare dake karamar hukumar Makoda Kano, wanda ake zargi da daure dan uwansa mai suna, Basiru Dankiri, da sarka a cikin wani daki wanda babu kulawa kirki kusan shekaru goma, ya tabbatar da cewa ya kai dan uwan nasa asibitin Dawanau don duba lafiyarsa.

Dandukulle ya ce lokacin da sukaje asibitin, sun shaidawa jami’an lafiyar duk abinda da suka sani, kuma sun basu shawarwarin kan yadda za su kula dashi.

Sai dai wanda ake zargin da daure dan uwan nasa, ya tabbatar da cewa har yanzu Basiru Dankiri, yana cikin dakin da yake kuma ya kwance shi daga sarkar da ya daureshi.

Mutanen garin Wailaren suna zargin Abdussalam Dandukuule, ya daure kaninsa dinne don ya mutu ya cinye gadonsa , wanda a cewarsu babu wata kulawa da ake bashi domin ko abincin kirki baya samu, inda wanda ake zargin ya musanta zargin.

A bangarensa Dandukulle, ya ce bai daure dan uwansa domin ya cutar da shi ba, yayi hakan ne saboda matsalar shaye-shaye da yake yi , kuma hakan ne ya jefa kaninsa cikin wannan yanayi na rashin lafiya.

Abaya wani Abokin, Basiru Dankiri , ya tabbatar da cewa abokinsa baya shaye-shaye kamar yadda yayan nasa ya fada, amma a shekarun baya sun taba zuwa sun kamo maciji wanda suke ganin shi ne sillar shigar basiru cikin rashin lafiyar.

Sai dai ya kara da cewa akwai babban yayansu wanda Allah ya yi wa rasuwa,  shi ne yake kula da Basiru kafin ya rasu har ya samu lafiya, amma bayan rasuwarsa sai Dandukulle ya daure shi, ya daina bashi kulawa ta abinci da magani wanda hakan yana daga cikin abundaya kara jefa shi cikin rashin lafiyar domin ko Magana baya samu balle abinci.

Haka zalika dagacin Garin Wailare Alhaji Badamasi Halilu, ya bayyana cewa akwai alamu na rashin gaskiya a tattare da yayansa kasancewar an yi alkawari dashi, amma yayi tafiyarsa sannan wata tsohuwar mata ta dinga tada sababi cewa babu wanda zai dauki Basiru Dankiri ya kaishi asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *