na neman mawaƙi Portable ruwa a jallo

Spread the love

Rundunar sojin Najeriya reshen jihar Ogun ta ayyana mawaƙi Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo saboda zargin sa da hannu a kai wa ofisoshin gwamnati hari.

A cewar wata sanarwa da runudnar ta fitar ranar Litinin, ana zargin Portable ne da jagorantar wani gungun ‘yandaba don kai hari kan jami’an ma’aikatar tsare birane ta jihar Ogun lokacin da suka je aiki yankin Ota na jihar.

Sanarwar ta ce an ga mahaifin Portable a wani wurin cin abinci da ke kusa da wurin, kuma ya faɗa wa mutane cewa ɗan nasa ba shi wurin.

“Sai dai jim kaɗan mawaƙin ya bayyana a wurin ɗauke da bindiga da sauran makamai kuma ya jagoranci kai hari kan jami’an hukumar,” a cewar ‘yansanda.

Rundunar ta ƙara da cewa ta kama tara daga cikin maharan, yayin da Portable ya gudu kuma yake ci gaba da ɓuya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *