Katota Ta Kawo Mota Ta SCID Kano Amma Babu Dukiyar Dake Ciki : Barista A.S. Bawa

Spread the love

Lauyan da yake zargin wasu jami’an hukumar Karota da dauke masa mota ba tare da saninsa ba, da kuma zargin sun sace masa kudi naira dubu 950, ya ce zai ci gaba da neman hakkinsa bisa doron doka da adalci har sai gaskiya ta yi halinta.

Lauyan mai suna, Barista Ahamd Sani Bawa, ya bayyana cewa duk da ya shigar da korafinsa, a ofishinsa kwamishinan yan sandan jihar Kano, da yanzu haka ake ci gaba da gudanar da bincike.

Sai dai ya ce wanda yake zargin ya ci zarafinsa ta hanyar duka, har yanzu ba a zo dashi sashin da ake gudanar da binciken ba, amma dai ya ce jami’an yan sandan suna iya bakin kokarinsu wajen gudanar da binciken kawai wasu daga hukumar Karotar suke neman mayar da hannun agogo baya.

 

Ya kara da cewa, an dauko motarsa daga hannun Kaota zuwa shelkwatar rundunar yan sandan Kano, kuma an bude ta a gabansa amma ba a samu dukiyarsa ba harda wani Agogo, da yake zargin an sace bayan an dauke motarsa.

‘’ wannan abun b azan barshi ba, zan ci gaba da bin hakki na ta hanyar doka’’.

Lauyan ya ce an kira su ranar Laraba, a sashin tattara bayanan sirri dake rundunar yan sandan jihar Kano, sai dai bangaren wadanda ake zargin ba su zo da wuri ba, inda suka dinga jan kafa sannan wanda yake zargi na farko kuma bai zo ba.

Sai daga karfe ya ce jami’an yan sandan sun gargade su, cewa ba a yin wasa da bincike don haka su zo da wanda ake zargi na farko bisa jagorancin lauyan hukumar Karotar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *