Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa ya ce ya yi fari ciki da kamen da hukumomin Finland suka yi wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar ƴan aware ta IPOB ta Najeriya, Simon Ekpa.
Cikin wani saƙo da kakakin ma’aikata tsaron ƙasar, Manjo Janar Tukur Gusau ya aike wa BBC ya ce babban hafsan tsaron ƙasar ya ce yana fatan kamen ya zama wani mataki na tisa ƙeyar Mista ekpa zuwa Najeriya don ya fuskanci shari’a.
A ranar Alhamsi ne hukumomin Finland suka kama Simon Ekpa tare da aika shi gidan yarin ƙasar, byan gurfanar da shi a kotu, kan zargin tunzura mutane su aikata ayyukan ta’addanci.
Kotun ta ce ta samu Simon Ekpa ne da laifin yaɗa aƙidu na ƴan aware a kafar sada zumunta, a ranar 23 ga watan Agustan 2021 a birnin Lahti na ƙasar ta Finland.