NAFDAC ta ƙwace haramtaccen maganin feshi na naira miliyan 20 a Sokoto

Spread the love

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya ta ƙwato magungunan feshi da basu da inganci da na bogi da kuma waɗanda aka haramta shiga da su ƙasar da kuɗin su ya kai naira miliyan 20 a kasuwannin jihar Sokoto.

Sanarwar da NAFDAC ta fitar ta ce ta kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a safarar kayan.

Hukumar ta ce ta yi nasarar kamen ne bayan bincike da kuma aikin haɗin gwiwa a tsakanin jami’anta da sauran jami’an hukumomin hana safarar ƙwayoyi.

NAFDAC ta kuma ƙona katon-katon na wani maganin feshi mai suna Endocoton Super, wanda ke ɗauke da sinadarin da ke da illa ga lafiyar jama’a da kuma muhalli.

Kasuwannin da hukumar ta ce jami’anta sun kai samamen sun haɗa da tsohuwar kasuwa da kasuwar Kara da kuma babbar kasuwar Sokoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *