Babban Dalilin matasa na yin tsayuwar daka wajen ganin tafiyar Tinubu da Kashim a zaben shekara ta 2027 ce fitilar nasarar Jam’iyyar APC.
Guda cikin masu rajin bayyana nagartar Kashim Shettima tare da goyon bayan ganin takarar Tinubu/Kashim ta tabbata, Alhaji Aminu Abubakar Boyi ne ya bayyana haka alokacin da yake jawabi ga dandazon matasa masu kishin cigaban tafiyar Kashim da Tinubu wanda aka gudanar a Kano.
Hon. Boyi yace maganar da Mai magana da yawun Shugaban Kasa Bayo Onanuga ya yi kan cewa sai bayan tsayar da dan takarar shugaban kasa ne shi wanda aka tsayar zai zabi mataimakinsa, wannan wata magana ce, abinda mujmke cewa shi ne halatan Tinubu ne Shugaban Kasa Kashim Shettima kuma shi ne mataimakinsa, don haka idan ba rami mai ya kawo maganar rami?
- Kotu ta aike da dan TikTok din da ke wanka a kan titi a Kano gidan yari
- Kotu ta aike da dan TikTok din da ke wanka a kan titi a Kano gidan yari
Yace kamata ya yi tunda dukkansu na kan karagar mulki ya zama dole duk inda aka ambaci Shugaban Kasa a ambaci mataimakinsa, kuma muna Jan hankalin masu wancan kulle kullen su sani duk wani yunkurin aje Mai Girma Kashim tamkar gayyatowa Jam’iyyar APC faduwa a zaben shekara ta 2027.
Boyi daganan sai ya bukaci matasa da masu goyon bayan Mai Girma Kashim kowa ya kara Jan damara domin kare kimarsa da muhibbarsa shi ne babban aikin da muka sa gaba, haka kuma muna nan muna shirin gudanar gagarumin taron da zamu gudanar domin Ci gaba da yayata manufofin alhairan Kashim Shettima.