Najeriya ba ta kai lokacin kafa ƴan sandan jihohi ba – Spetan Ƴan sanda

Spread the love

Babban spetan ƴan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya ce ƙasar ba ta kai ta kafa rundunar ƴan sandan jiha ba duk da ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin wani taron tattaunawa game da kafa rundunar ƴan sandan jiha da aka gudanar a Abuja, babban birnin ƙasar da aka yi wa taken “Hanyoyin samun zaman lafiya: Sake fasalin ƴan sanda a Najeriya”.

Babban Spetan ƴan sandan ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai lokacin da za ta kafa rundunar ƴan sandan jihohi ba, in ji shi wanda ya samu wakilcin AIG Ben Okolo a taron da kakakin majalisar wakilan Najeriya, Tajuddeen Abbas ya shirya.

Babban spetan ya ce akwai yiwuwar wuce gona da iri daga gwamnatocin jihohi.

“Gwamnonin jihohi na iya amfani da ƴan sandan domin buƙatarsu ta siyasa ko ta ƙashin kai tare da murƙushe haƙƙoƙin bil adama da tsaro.”

Sai dai ya bayar da shawarwari na yadda za a inganta ayyukan ƴan sanda wajen haɓaka tsaro a ƙasar.

“Da farko, hukumar tsaron Civil Defence da hukumar kare afkuwar haɗura su kasance sashe aƙarƙashin rundunar ƴan sandan Najeriya,” in ji shi.

A cewar babban spetan, akwai buƙatar a ƙara yawan jami’an tsaron da ake ɗauka aiki duk shekara. Da kuma basu horo, abin da ya ce na da muhimmanci wajen tabbatar da tsaro a Najeriya.

A taron da ya samu halartar manyan jami’ai a Najeriya, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan yana ganin duk da ƙalubalen da ake fuskanta, kafa rundunar ƴan sandan jihohi a Najeriya abu ne na dole.

Ya ce ƙaruwar sace-sacen mutane da sauran laifuka ya sa kafa rundunar ƴan sandan jihohi ya zama wajibi a halin da ake ciki a Najeriya.

Ba ya ga Jonathan, taron ya samu halarta mataimakin shugaban ƙasa Kassim Shettima inda ya bayyana ƙudirin shugaba Bola Tinubu na inganta ayyukan ƴan sanda a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *