Gwamnatin Najeriya ta cimma yarjejeniya da ƙasar Kuwait don fara zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin ƙasashen biyu.
Ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Mista Keyamo ya ce ya rattaɓa hannu a madadin gwamnatin Najeriya don cimma yarjejeniyar jigilar jiragen sama tsakanin ƙasashe biyu, don bayar da dama ga kamfanonin jiragen sama da aka keɓe don gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci, wanda ya shafi jigilar fasinjoji da kaya.
A cewar Keyamo, an rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a taron tattaunawa kan harkokin sufurin jiragen sama na ƙasashen duniya (ICAN) da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta ƙasashen duniya (ICAO) ta shirya a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.
“Wannan zai bunƙasa harkokin kasuwanci da yawon bude ido da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Ni da tawagata za mu ci gaba da tattaunawa kan hanyoyi daban-daban tare da ƙasashe daban-daban da ke nan don halartar wannan taron na ICAO na shekara-shekara har zuwa karshen mako, ” in ji Keyamo