Najeriya da Qatar sun cimma yarjejeniyoyin hadin gwiwa

Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Tinubu da sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi da za su bude kofar inganta muhimman fannoni tsakanin kasashen biyu.

Bangaren da yarjejeniyoyin za su shafa sun hadar da fannonin ilimi da kasuwanci da inganta zuba jari, da sama wa matasa ayyuka da harkar ma’adinai da yawan bude ido da wasanni.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya ce an cimma yarjejeniyar ce a fadar sarkin Qatar.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce a shirye kasarsa take don yin maraba da masu zuba jari, yana mai cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi na inganta zuba jari a kasar.

Ya ce babban karfinmu shi ne mutanenmu. karfinmu ya dogara kan matasanmu. suna da karfi , da fikira da yarda da kansu,” in ji shugaban na Najeriya.

Ya kara da cewa matasan kasar na da ilimi kuma suna da fikirar neman sana’a a duk inda take.

Wasu Yan Daudu Sun Yi Wa Ofishin Hisbah Rotse Tare Da Kwantar Da Tutocinsu A Unguwar Bachirawa Kano.

Shugaba Tinubu ya nada ministan kudi da na tattalin arziki, mista Wale Edun a matsayin wanda zai jagoranci tawagar gwamnatin Najeriya da za ta tattauna da hukumomin Qatar wajen gano bangarorin da za a zuba jarin da aiwatar da shi, don ciyar da kasar gaba.

Shugaba Tinubu dai na ziyarar aiki a kasar Qatar tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *