Najeriya da wasu kasashen Afirka sun fuskanci matsalar katsewar internet

Spread the love

Wasu kasashen Afirka biyar ciki har da Najeriya sun fuskanci matsalar katsewar intanet.

An samu rahotonnin katsewar intanet din a kasashen Afirka ta Kudu da Najeriya da Ivory Coast da Laberiya da Ghana da kuma Burkina Faso.

To sai har ya zuwa yanzu ba a bayyana dalilin katsewar intanet din ba

“An samu bambanci dangane da lokacin katsewar intanet din, wanda ya faro daga arewa zuwa kudancin Afirka”, in ji Cloudflare Radar, wani da ke samar da bayanai kan sadarwar intanet.

Sadarwar intanet a kasar Ivory Coast ya ragu da kashi hudu da safiyar ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin Netblocks, wanda ke lura da tsaron intanet da sadarwar intanet.

A Laberiya kuma an samu raguwar da kashi 17, yayin da a Benin ya ragu da kashi 14, Ghana kuma 25, kamar yadda Netblocks ya bayyana.

A Afirka ta Kudu, Vodacom ya ce “Abokan huldarmu na fuskantar matsalar katsewar intanet sakamakon matsalar wani kebul da ke karkasin teku”.

Shi ma kamfanin Cloudflare ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa yana fuskantar babbar matsalar katsewar intanet a Gambiya da Guinea da Liberia da Ivory Coast da Ghana da Benin da kuma Jamhuriyar Nijar.

Yan Jaridar Portugal Sun Fara Yajin Aiki Karon Farko Cikin Shekaru 42.

Yar’Adua ya zama sabon shugaban kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya

Kamfanin Microsoft, ya ce za a dauki tsawon sa’o’i 12 kafin ya iya dawo da zirga-zirgar intanet ga abokan cinikinsa.

A watan da ya gabata, an sami yanke igiyoyi da yawa a cikin Bahar Maliya wanda ya shafi kusan kashi 25% na bayanan da ke gudana tsakanin Asiya da Turai.

An nuna damuwa game da igiyoyin da mayakan Houthi da ke aiki a tekun Bahar Maliya ke kaiwa hari. Sai dai sun musanta kai hari kan layin.

An sha samun katsewar wayoyin sadarwar Internet na karkashin ruwa a baya, amma da alama a wannan karon lamarin babba ne, inji Isik Mater, daraktan bincike na cibiyar ta Netblocks.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *