Najeriya ta ƙara kuɗin yin takardar fasfo

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta ƙara kuɗin mallakar takardar tafiye-tafiyen ƙasashen waje na ƙasar, wato fasfo, inda sabon ƙarin zai fara aiki daga ranar ɗaya ga watan Satumban 2024.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar shige da fice ta ƙasar, DCI Kenneth Udo ya fitar, ya ce ƙarin na cikin yunƙurin gwamnatin na tabbatar da ingancin fasfo na ƙasar.

Ya ce daga wannan ƙarin, fasfo mai shafi 32 wanda yake yin shekara 5, wanda a baya ake yin sa kan naira 35,000, yanzu ya koma naira 50,000; sannan fasfo mai shafi 64, mai wa’adin shekara 10, wanda a baya ake samun sa a kan naira 70,000, yanzu ya koma Naira 100,000.

Sai dai sanarwar ta ƙara da cewa ba a ƙara kuɗin na fasfo ba ga ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje.

Da take bayar da haƙuri a kan matakin, da kuma damuwar da lamarin zai iya haifarwa, hukumar ta tabbatar wa ƴan Najeriya cewa a shirye take da cigaba da yin aiki tuƙuru domin yin abin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *