Ministan tsaron Najeriya ya ce ƙasar ta samu dukkan cancantar da ake buƙata ta samun zama mamba a Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
Da yake gabatar da jawabi yayin wani taro a birnin New York na Amurka, Mohammed Badaru ya ce Najeriya ta ba da gudummawar kiyaye zaman lafiya a ƙasashe 41 tare da tura dakaru sama da 200,000.
Taron mai taken “Enhancing Multilateralism for International Peace and Security” game da zaman lafiya a duniya, wani ɓangare ne na taron babban zauren MDD na 76 da ake yi a Amurkar.
“Tun daga fara tura dakarunmu a ƙasar Kongo a shekarar 1960, Najeriya ta shiga ayyuka 41 na kiyaye zaman lafiya a duniya,” in ji shi.
Ministan ya kuma nemi a yi gyara a tsarin kwamatin domin bai wa nahiyar Afirka kujerar wakilci ta dindindin. Yanzu haka ƙasashen Amurka, da Birtaniya, da China, da Faransa, da Rasha ne kaɗai ke da wannan matsayin.