Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta doke takwararta Black Stars ta Ghana a wani wasan sada zumunta da suka fafata yau Juma’a a kasar Morocco.
An dai tashin wasan ne 2–1, inda Najeriya ta yi galaba a kan makwabciyarta da ke Yammacin Afirka.
Dan wasan Najeriya Cyriel Dessers ne ya ci kwallon farko a bugun fenariti a minti na 38, sannan a minti na 84 kuma Ademola Lookman ya zura tasa kwallon.
Ghana ta ci kwallonta ne da bugun fenariti ta hannun dan wasanta Jordan Ayewa gab da ana kusan tashi a wasan.
Daya daga cikin ’yan wasan bayan Ghana ya Jerome Opoku ya samu jan kati a minti na 56 da soma wasan.
Haduwar kasashen biyu na zuwa ne kasa da watanni biyu bayan kammala Gasar Kofin Nahiyyar Afirka na AFCON da aka yi a Ivory Coast wacce ta lashe kofin.
Najeriya ta kai wasan karshe a gasar yayin da aka cire Ghana tun a zagayen rukuni-rukuni, lamarin da ya yi sanadin korar mai horar da ‘yan wasan kasar.
ya nuna sau 56 Najeriya da Ghana suka kara a fagen kwallon kafa a gasa daban-daban da wasannin sada zumunci.
Kazalika, Taiwo Awoniyi da Tyronne Ebeuhi da Gabriel Osho duk ba su samu halartar wasan na sada zumunci ba.
A bangaren Ghana, fitaccen dan wasan kasar Thomas Partey, shi ma bai samu zuwa wasan ba.