Najeriya ta kaddamar da mizanin gano halayyar masu hulda da kafafen yada labarai

Spread the love

Ministan yada labarai da wayar da kai na Najeriya, Alhaji Muhammad Idris Malagi ya bukaci shugabannin hukumomi masu yada labarai da kafafen yada labarai na kasar da su kyautata aikinsu ta hanyar amfani da sabon ma’aunin fahimtar hallayar masu hulda da kafafen watsa labarai musamman rediyo da talbijin na kasar.

Ministan dai na wannan bayani ne a lokacin kaddamar da wannan sabon mizani wanda kwararru da masana suka kwashe dogon lokaci suna bincike kuma suka mika shi ga gwamnatin tarayya.

Mizanin mai shafi 182 wanda zai maye gurbin tsohon tsarin ya mayar da hankali ne kan yawan mutanen da suke mu’amila da kafafen watsa labaran kasar.

Ministan ya yi kira ga shugabannin gidajen watsa labarai da hukumar tallace-tallace da su ci moriyar tsarin ta hanyar sanin hakikanin mutanen da ke mu’amila da su, inda kuma hakan zai ba su kudin shiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *