Najeriya ta sanya harajin dole ga kamfanonin da ke ɗaukar ma’aikata daga ƙetare

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta sanya harajin dole na shekara-shekara ga kamfanonin da ke ɗaukar ma’aikatan ƙasashen waje.

Gwamnatin ta buƙacin kamfanonin su riƙa biyan harajin dala 15,000 ga kowane darakta, da kuma dala 10,000 daga sauran ma’aikata.

Shugaban ƙasar Bola Tinubu, wanda ke cikin matsin lambar inganta tattali arzikin ƙasar, ya ce matakin zai ƙarfafa wa kamfanonin ƙasashen waje gwiwa wajen ɗaukar ‘yan ƙasar aiki.

Dama dai kamfanonin ƙasashen waje na biyan dala 2,000 a kowace shekara domin samun izinin zama a ƙasar ga ma’aikatansa ‘yan ƙasashen waje.

A yanzu kuma za su biya ninki biyar na wannan kuɗi, idan suna son ci gaba da aiki da ma’aikatansu ‘yan ƙasashen wajen.

Yan sanda da mafarauta sun kuɓutar da mutum 49 a Taraba

Yan Sandan Kano sun cafko mutum na 2 da ake zargi da laifin garkuwa da kuma kisan kai

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gwamnati ba ta ɗauki matakin don dankwafe masu zuba jari a ƙasar daga ƙetare ba.

Ɗaya daga cikin alƙawuran da shugaban ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe shi ne mayar da Najeriya ƙasar da za ta ja hankalin masu zuba jari daga ƙetare.

To sai dai wannan mataki zai sa da dama daga kamfanonin su ƙaurace wa zuwa ƙasar.

Matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar matsin tattalin arziki mafi muni a tarihi, da ake ganin an samu sakamakon tsare-tsaren gwamnati ciki har da cire tallafin man fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *