Najeriya ta yi asarar dala biliyan 200 a almundahanar kwangiloli – MacArthur

Spread the love

Gidauniyar MacArthur ta bankaɗo cewa Najeriya ta yi asarar kuɗi sama da dala biliyan ɗari biyu, a tsakanin shekarar 1970 zuwa 2008, sakamakon cin hanci da rashawa da almundahana da ake tafkawa ta hanyar bayar da kwangiloli.

A cewar Gidauniyar MacArthur asarar ta samo asali ne daga aringizon kuɗaden kwangiloli da ha’inci wajen sayar da ƙadarorin gwamnati da kuma satar arzikin ƙasa.

Gidauniyar ta MacArthur ta gano cewa, kwangilolin da ma’aikatun gwamnati kan bayar wata babbar ɓarauniyar hanya ce da kuɗaɗen Najeriya ke ta zurarewa shekara da shekaru, kamar yadda shugaban gidauniyar a Abuja, Dakta Kole Shettima ya shaida wa BBC.

Ofishin babban mai binciken kuɗi na Najeriya a watan Nuwamba ya fitar da wani rahoto da ya banƙado badaƙalar kwangiloli da ta kai kusan naira biliyan 200 a ma’aikatu da hukumomin gwamnati da dama na Najeriya tsakanin 2020 zuwa 2021.

Shugaban Gidauniyar MacArthur ya ce bincikensu ya gano yawan kuɗaɗen da ƙasar ta yi hasara cikin kusan shekaru 40 daga bayanan da suka samu ne daga hukumomin gwamnatin Najeriya.

Kuma a cewarsa an fi tafka cin hanci da rashawa a Najeriya ta hanyar bayar da kwangiloli.

“Kusan kashi 70 cikin 100 na cin hanci da rashawa a Najeriya yana faruwa ne saboda hanyoyin da ake bayar da kwangila a ƙasar domin ma’aikatun gwamnati ba su bin tsarin da ya kamata su bi na bayar da kwangiloli,” in ji Dakta Kole Shettima.

Ya ƙara da cewa girman matsalar ta kai wani lokaci har kamfanonin bogi ake samarwa kuma a ƙirƙiri kwangila domin su.

Shugaban Gidauniyar MacArthur ya jaddada muhimmancin tabbatar da gaskiya da adalci a dukkanin harkokin da suka shafi kwangiloli a ƙasar, ta hanyar tabbatar da sauyi da kuma sa ido domin daƙile matsalar rashawa da ta yi katutu a harakokin kwangiloli a Najeriya.

Ya ce cin hanci da rashawa babbar illa ce musamman karkatar da kudaden da ya kamata a yi muhimman ayyukan ci gaban ƴan ƙasa.

Shugabannin ƙungiyoyin fararen hula da ke yaƙi da rashawa a Najeriya kamar shugaban ƙungiyar CISLAC, kuma wakilin kungiyar Transparency International a Najeriya, Awwal Musa Rafsanjani ya ce wadannan bayanai ba abin mamakai ba ne a Najeriya.

“Mun daɗe muna cewa facaka da kuɗaɗen al’umma ta hanyar bayar da kwangilolin bogi da ƙara kuɗi a kwangilolin, don haka ba mu yi mamakin wannan rahoton ba illa ya ƙara jaddada abin da muka daɗe muna magana a kai.” In ji Rafsanjani.

Ya ce duk da akwai doka ta bayar da kwangila a Najeriya amma ba a aiki da ita wajen bayar da kwangiloli a ƙasar.

Masana dai sun yi nuni cewa shawo kan irin wannan gagarumar matsala ta cin hanci da rashawa da kuma almundahana, dole sai masu ruwa da tsaki da sauran al’ummar sun haɗa hannu ta hanyoyi daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *