Gwamnatin Najeriya ta aika sakon ta’aziyya tare da jaje ga shugaban ƙasar Rasha Vladmir Putin, kan harin da aka kai wani gidan rawa da ke kusa da birnin Moscow.
Cikin wani sakon X da ya wallafa, Ministan harkokin Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar ya ce Najeriya da mutanenta na jajantawa Rasha kan kisan mutanen da aka yi wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, da kuma gwamman da aka jikkata.
“Gwamnati da mutanen Najeriya na nuna alhini ga mutanen da wannan mummunan hari ya rutsa da su, muna fatan rahama ga wadanda suka mutu, da fatan samun sauki cikin gaggawa ga mutanen da suka jikkata,” in ji sakon na X.
A gefe guda ma China da India duk sun aika sakonsu na jajantawa ga Putin da mutanen Rasha baki daya.
Gwamnan Kano ya yi watsi da yadda tsarin raba abincin azumi a jihar
Matsalar Tsaro Ta Sake Dawowa A Bauchi
Rahotanni na cewa adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai wani gidan rawa a Rasha a daren jiya ya kai 115 kamar yadda hukumar bincike ta ƙasar ta bayyana.
Kamar yadda ta bayyana a wani sakon manhajar Telegram da ta aika, tawagar da take lura da lamarin ta ce, masu aikin agajin gaggawa da ke duba ɓaraguzan ginin sun sake gano gawarwaki da dama yayin aikinsu a zauren.
“Adadin a yanzu ya haura 115,” tana cewa kuma har yanzu ana ci gaba da bincike.