Najeriya za ta daina sayo mai daga waje a watan Yuni – Dangote

Spread the love
DANGOTE
DANGOTE

Matatar man Dangote da ke jihar Legas a Najeriya ta ce kasar za ta daina sayen man fetur daga waje a watan Yuni, lokacin da matatar za ta fara aiki.

Mai matatar, Alhaji Aliko Dangote shi ne ya bayyana haka a taron kolin shugabannin kamfanoni na Afirka ranar Juma’a a Kigali, babban birnin Rwanda.

Hamshakin attajirin ya ce, matatar za ta samar da man da ake bukata a cikin gida ba ga Najeriya ba kadai har ma da sauran kasashen yankin Afirka ta yamma.

Dangote ya ce, a cikin watan Yuni, wato nan da mako hudu zuwa biyar, ba wani mai da Najeriya za ta rika saye daga waje.

Bayan man fetur, ya ce matatar za ta kuma samar da isasshen man dizil ga Afirka ta yamma da ma Afirka ta tsakiya.

Haka kuma ya ce, matatar za ta iya samar da isasshen man jirgin sama ga nahiyar Afirka gaba daya, har ma ta fitar da shi zuwa kasashen Brazil da Mexico.

Attajirin wanda ya fi kowa kudi a Afirka ya kuma bugi kirji dacewa, nan da shekara uku zuwa hudu nahiyar Afirka ba za ta sake sayen takin zamani daga waje ba, domin matatar za ta wadata nahiyar da takin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *