Najeriya za ta haɗa gwiwa da Libya don daƙile yaɗuwar ƙananan makamai

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta haɗa gwiwa da Libya domin daƙile yaɗuwar ƙananan makamai.

Ministan tsaron ƙasar, Muhammad Badaru Abubakar shi ya bayyana haka ranar Lahadi, yayin wata tattaunawa da wakilin gwamnatin ƙasar Libya, a wani ɓangare na karfafa matakan tsaro, rage tu’ammali da ƙwayoyi da kuma ɗorewar ƙasashen biyu.

Badaru ya tabbatar da cewa Najeriya a shirye take wajen ci gaba da aiki da sauran ƙasashen Afrika da kuma karfafa haɗin gwiwa a matakin yanki da kuma na ƙasa da ƙasa.

A cewarsa, safarar ƙananan makamai ba ta san kan iyaka ba kuma ba ta mutunta dokoki, inda ya ce ya zama tilas a haɗa kai don aiki tare.

Tun da farko, shugaban tawaga kuma wakilin hukumar tsaro ta ƙasar Libya, Janar Mohammed M.M Azain, ya bayyana cewa sun kawo ziyara Najeriya ne don tattauna matsalolin rashin tsaro da ke addabar ƙasashen da kuma samar da hanya ta daƙile yaɗuwar ƙananan makamai.

Ƙasashen biyu sun yi alkawarin ci gaba da ɓullo da hanyoyin daƙile yaɗuwar ƙananan makamai da kuma safarar ƙwayoyi daga LibyaLibya zuwa Najeriya, saboda ɗorewar ƙasashen biyu da kuma kare jama’arsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *