Nasarorin Da Wakilin Tarayya Na Mazabar Rano, Kibiya, Bunkure Ya Samar Cikin Shekara 1

Spread the love

Yayin da a wannan Rana daukacin Wakilan majalisun Tarayya na kasa ke cika shekara guda da karbar rantsuwar kama aiki, Wakilin Kananan Hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure RT Hon Kabiru Alhassan Rurum ya bayyana nasarorin da Ayyukan daya samu nasarar gudanarwa Al’ummarsa a wannan shekarar(2023-2024).

Hon Rurum yace duk da runtsi na mashashsharar tattalin Arziki da tsadar rayuwa da wahalar da ‘Yan Kasa ke fuskanta a cikin wannan shekarar ya samarda kusan trela 8 ta kayan abinci daya hadarda fiye da trela biyar ta Shinkafa da guda ta Gero sai Kuma Taliya da tuni an rabarwa Al’ummar maxabun nasa don rage musu matsalar Yunwa da rashin Abinci.

Haka Kuma Wakilin a taron manema labarai Daya gudanar a Yau Alhamis Wanda Mai taimaka masa Kan harkokin yada labarai Fatihu Yusuf Bichi ya Jagoranta, yace a cikin shekarar nan guda fiye da Matasa 13 ya samarwa aiki a Ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya sai Kuma fiye da 30 da aka samarwa gurbin aikin sojin sama da (NDA Kaduna) da kuma wasu matasan 5 da aka samarwa gurbin aiki da rundunar Civil Defense da Kuma 7 da suka sami aiki da hukumar kula da shige da fice(Immigration) da wasu matasan kusan 36 da aka samarwa aikin dan Sanda duk a yankin Kananan hukumomin na Rano, Kibiya da Bunkure.

A bangaren Dalibai kuwa, Rt Hon Rurum ya samarda gine ginen Ajujuwa a garuruwan Jan Garu da Gwaneri a cikin shekarar nan sai Kuma daukar nauyin biyan form na Jamb ga Dalibai kusan 300 bayaga kusan Dalibai 1,000 daya biyawa Kudin Jarrabawar Neco wadanda suka Fadi Jarrabawar Qualifying a shekarar bara 2023, sannan kuma kusan dalibai 160 ‘Yan Asalin kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure dake karatu a Jami’ar Bayero ta Kano da na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria suka Karbi tallafin naira dubu 50 -50 Kowannensu.

A fannin ayyukan raya kasa ma dai cikin wannan shekara Rurum din ya samarda manyan hanyoyi guda 3 Kibiya zuwa Bacha, da hanyar data tashi daga gidan Murabus zuwa Kasuwar Dila a Rano Kuma tuni ana aikin wasu hanyoyin yanxu haka..

Bayaga tallafin kudi daban daban Daya bayar ciki harda rabon naira miliyan 46 da akayi baya bayan nan ga Al’ummar mazabun nasa, Rurum ya sanya fitilu masu Amfani da hasken rana guda 450 a garuruwa daban daban sai Kuma kudiri samar da makarantar Sakandiren kwana ta mata ta sojin sama daya gabatar a zauren majalisar Wakilan ta kasa da kuma kudirin kara karfafa tsaro da kayan aiki a gidajen gyaran halin da ake dasu a kasarnan daya gabatar a zauren nasu da nufin kawo karshen ballewar da daurarru keyi a gidajen gyaran hali ko kai hare-haren kubutar da su da ‘yan ta’adda keyi.

A karshe Muna kira ga Al’ummar wadannan Kananan Hukumomin su cigaba da baiwa dan majalisar hadin kai da goyon baya da yi masa Addu’oin samun nasarar cigaba da gabatar musu da ayyukan raya kasa da Cigaban Al’umma..

Mungode.

*Fatihu Yusuf Bichi*
*S A Media to Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum*
*Member Representing Rano, Kibiya & Bunkure Federal Constituency*
*13/6/2024.*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *