NCAA za ta hukunta kamfanonin jirgin sama da ba su mutumta ƙa’idar lokaci

Spread the love

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya, NCAA ta yi gargaɗin cewa za ta hukunta kamfanonin sufurin da ke yaudarar matafiya a kan lokacin tafiyar jirage.

Muƙaddashin daraktan hukumar, Chris Najomo, ya ce hukumar ba za ta lamunci rashin cika alƙawari da kuma kiyaye ƙa’idojin sufurin jirgin sama ba.

Ya yi gargaɗin cewa kamfanonin da suke saɓa ƙa’idojin za su fuskanci hukunci mai tsanani, kamar yadda doka ta yi tanadi.

Hukumar ta ce ta yi tanadi mai inganci domin sauƙaƙe yadda ake mallakar lasisin gudanar da kamfanonin jiragen sama a Najeriya, da kuma kaucewa kura-kuran baya.

“NCAA ta na fatan ganin hakan zai sa kamfanonin jiragen su tashi tsaye domin gudanar da ayyukan su yadda ya dace” inji Chris Najomo.

NCAA ta jaddada cewa babu wani dalili da zai hana kamfanonin jiragen sama gudanar da ayyukan cikin tsari kamar yadda ake yi a sauran ƙasashen duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *