Rundunar ‘yansandan Najeriya ta tura ƙarin dakaru na musamman yankin ƙaramar hukumar Gwoza na jihar Borno domin tsaurara tsaro bayan harin bama-bamai da ya kashe mutum 18 ranar Lahadi.
Da yake miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar jihar a yau Litinin, Sufeto Janar na ‘Yansadan Najeriya IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya ba da umarnin tura ƙwararrun dakarun rundunar a ɓangaren bama-bamai.
“Sashen abubuwan fashewa (EOD) na rundunar tare da haɗin gwiwar sojojin Najeriya na cigaba da aikin dudduba wurin don tabbatar da cewa babu sauran barazana,” a cewar wata sanarwa da kakakin runundar Olumuyiwa Adejobi ya fitar.
Lamarin ya faru ne lokacin da wasu ‘yan ƙunar bakin wake suka tayar da bama-baman da ke jikinsu a cikin mahalarta wani taron biki a ƙaramar hukumar Gwoza.
Gwamnatin jihar ta ce maharan sun yi amfani da “girman jihar ne da kuma ƙarancin tsaro a kan iyakoki” kafin su kai harin.